✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Coronavirus: Majinyata 321 suka warke a Legas

Zuwa yanzu majinyata 321 ne suka warke daga cutar coronavirus a jihar Legas tun bayan barkewar annobar a jihar. A wata  sanarwar da gwamnan jihar…

Zuwa yanzu majinyata 321 ne suka warke daga cutar coronavirus a jihar Legas tun bayan barkewar annobar a jihar.

A wata  sanarwar da gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu, ya fitar a ranar Talata, 5 ga watan Mayu a shafinsa na twitter, ya shaida cewa an samu karin majinyata 60 da suka warke aka kuma sallame sun koma cikin iyalansu.

Ya ce, 40 daga cikin majinyatan maza ne, 20 kuma mata, da aka sallama daga cibiyar kula da majinyatan da ke Yaba, da Eti-Osa, da kuma ta Ibeju-Lekk.

” Majinyata 31 daga cibiyar kula da masu jinyar cututtuka masu yaduwa ta Yaba aka sallame su, yayin da aka sallami  19 daga cibiyar da ke Ibeju-Lekki, sai  10 daga cibiyar da ke Eti-Osa. daukacin su sun warke sarai sun kuma koma cikin iyalansu” inji gwmana Sanwo-Olu.

Jihar Legas wacce ita ke da yawan majinyata cutar coronavirus  a Najeriya ta sallami mutum 321 da suka warke.