✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus ta kama karin mutum 675, ta kashe 6 a Najeriya

A ranar Alhamis an samu karin mutum 675 da suka kamu da cutar Coronavirus yayin da kuma ta kashe karin mutum 6 a fadin Najeriya.…

A ranar Alhamis an samu karin mutum 675 da suka kamu da cutar Coronavirus yayin da kuma ta kashe karin mutum 6 a fadin Najeriya.

Hukumar Dakile Cututtuka masu Yaduwa a Kasar NCDC ce ta sanar da hakan cikin alkaluman da ta fitar kamar yadda ta saba duk rana.

Alkaluman sun nuna an samu karin mutum 675 da suka harbu da cutar a jihohi 16 da suka hada da Legas (128), Abuja (183), Kaduna (85), Kwara (57), Katsina (50), Filato (42), Ribas (39) da Kano (33).

Sauran jihohin su ne Ondo (21), Ogun (17), Bauchi (10), Sakkwato (5), Edo (2), Ekiti (1), Bayelsa (1), and Delta(1).

Ya zuwa yanzu dai cutar ta harbi mutum 71,344 a Najeriya yayin da tuni an sallami mutum 65,474 daga cibiyoyin killace masu cutar bayan samun waraka.

Da wannan sabbin alkaluma da aka fitar, har ila yau jihar Legas ce a kan gaba ta fuskar yawan masu cutar da suka kai 24,366 sai kuma Abuja a mataki na biyu da mutum 7,899 yayin da jihar Filato ta tuke a mataki na uku da mutum 3,979.

Haka kuma alkaluman sun nuna jimillar wadanda cutar ta kashe a fadin kasar sun kai 1,190 tun daga bullarta a watan Fabrairun 2020 zuwa yanzu.