✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus ta sake kashe mutum 3 a Najeriya

A ranar Talata an samu karin mutum uku da suka mutu sakamakon cutar coronavirus kamar yadda alkaluman Hukumar Dakile Cututtuka masu yaduwa a kasar NCDC…

A ranar Talata an samu karin mutum uku da suka mutu sakamakon cutar coronavirus kamar yadda alkaluman Hukumar Dakile Cututtuka masu yaduwa a kasar NCDC suka nuna.

Kazalika alkaluman sun nuna cewa an samu karin mutum 281 da suka kamu da cutar a Najeriya.

Alkaluman da NCDC ta fitar a ranar 1 ga watan Dasumba sun nuna jimillar wadanda cutar ta kashe a fadin kasar sun kai 1,176 tun daga watan Fabrairun 2020 da ta bulla.

Haka kuma karin mutum 281 sun harbu da cutar a jihohi 13 da suka hada Legas (123), Abuja (64), Kaduna (38), Imo (15), Ribas (11), Filato (8), Ogun (5), Bayelsa (4), Kwara (4), Bauchi (3), Edo (3), Kano (2) da Osun (1).

Ya zuwa yanzu dai jimillar wadanda cutar ta harba ya zama 67,838 kuma daga cikinsu an sallami mutum 63,430 daga cibiyoyin killace masu cutar bayan sun samu waraka.

Da wannan sabbin alkaluma da aka fitar, jihar Legas ce a kan gaba ta fuskar yawan masu cutar da suk kai 23,410 sai kuma Abuja a mataki na biyu da mutum 6,868 yayin da jihar Filato ta biyo baya a mataki na uku da mutum 3,877.