✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Coronavirus: Yadda za ku kare kanku daga mazambata

Tun bayan bullar cutar coronavirus a Najeriya, mutane ke samun sakwanni ta kafofin sadarwa na zamani game da cutar. A irin wannan yanayin ne wasu…

Tun bayan bullar cutar coronavirus a Najeriya, mutane ke samun sakwanni ta kafofin sadarwa na zamani game da cutar.

A irin wannan yanayin ne wasu ’yan damafara suka ga dama ta samu da za su yi wa bayin Allah zamba cikin aminci, har ta kai Babban Bankin Najeriya (CBN) yin gargadi da a kiyaye.

Malam Abdullahi Salihu Abubakar, wanda aka fi sani da Baban Sadik, masani ne a kan harkar sadarwa ta zamani, kuma ya yi wa Aminiya bayani a kan dalilan da suka sa bata-gari ke amfani da wannan lokaci don aikata aika-aika, da salon da suke amfani da shi, da kuma yadda mutane za su kare kansu daga fadawa tarkon mazambata.

Dalilan yawaitar zamba ta intanet yanzu

 1. Hukumomi a matakan jiha da tarayya sun killace jama’a a gidaje ko sun takaita hadahada don hana yaduwar cutar coronavirus.
 2. Saboda dalili na sama, galibin ma’aikatan kamfanoni da hukumomi sun koma amfani da hanyar sadarwa ta zamani don ci gaba da gudanar da ayyuka daga gidajensu.
 3. Makarantu sun rufe; a wasu kasashe galibin dalibai na daukar darasi ta hanyar Intanet ne da sauran na’urorin sadarwa.
 4. A wasu kasashen, galibin asibitoci na lura da marasa lafiyar da cutarsu ba ta yi tsanani ba ta hanyoyin sadarwa, don rage cunkoso a asibitoci.
 5. Hukumomi na amfani da kafafen sadarwa don bai wa jama’a tallafin kudi ko abinci ko rage radadin zaman gida da karancin abinci yayin killace kai.

Hanyoyin da mazambata ke amfani dasu

Saboda haka mazambata suka yi wuf suka shiga amfani da wannan dama don yin damfara ta hanyoyi kamar haka:

 1. Sakwannin tes: Aika sako da sunan banki don karbar mahimman bayanan masu ajiya da sunan za a ba su tallafi. Da kuma yada sakwannin bogi don jefa tsoro ko motsa kwadayin mutane kan tallafin gwamnati.
 2. Imel: Aika sakwanni ta amfani da shafukan bogi na manyan bankunan Najeriya don yaudarar jama’a zuwa shafukan da suka kirkira don sace bayanansu na banki.
 3. Kiran waya: Da sunan su ma’aikatan banki ne dake bayar da tallafin gwamnati. Suna son karbar lambar BVN ne da ranar haihuwa da lambar asusun ajiyar banki.
 4. Yaudara ta hanyar abota: Wannan shi ake kira “Social Enginerring“. Ya kunshi kulla alaka da mutane a kafafen sada zumunta—Facebook, WhatsApp, Twitter, Instagram—don tatsar bayanan jama’a ko yada labaran karya don jefa tsoro ko motsa kwadayin son kudi a zukatan mutane.
Abdullahi Salihu Abubakar
Malam Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik) ya ce a guji ba da bayanai ta waya

Yadda za ku kare kanku

Za ku iya kare kanku daga fadawa tarkon ’yan damfara ta wadannan hanyoyin:

 1. A guji aika lambar asusun ajiya ko BVN ko ranar haihuwa zuwa wani layin waya da wani ya bukata haka kawai. Babu bankin da zai taba neman lambar BVN dinka ko ranar haihuwarka ta hanyar sakon tes. Karya ce.
 2. A guji latsa wani adireshi (ko rariyar likau) da wani ya aiko ta Imel don isa ga wani bayanin da ya ce akwai fa’ida a ciki. A takaice ma, duk wanda ya aiko maka sakon Imel kuma ba ka san shi ba, kai ko ka san shi, muddin ya bukaci wasu bayanai na banki daga gareka, ko ya ce ga wani adireshi nan ka shiga don sanya bayanai, kada ka yi. Yaudara ce.
 3. A guji ba da bayanai ta hanyar kiran waya da wani ya yi ya ce shi ma’aikacin banki ne. Da zarar ya fadi haka ma kada a tsaya dogon zance da shi, a katse wayar. Mayaudari ne.
 4. A guji abota da wadanda ba a sani ba a kafafen sada zumunta. Duk wata hira da za ta kai ga neman lambar banki ko BVN misali, a yi maza a katse ta. Haka duk wani hoto ko wani labari da za a kawo da sunan gwamnati za ta bayar da tallafi, ya kamata a tantance labarin kafin a yi wani yunkuri.

Hanyoyin Tantancewa

Ana iya tantance labaran karya ta hanyoyi kamar haka:

 1. Idan zallan hoto ne aka ce ga wani abu ya faru a gari kaza misali, ko ga wasu ana ba su tallafi, ana iya neman tabbaci ta hanyar duba kafafen yada labaran cikin gida—jaridu da gidajen rediyo ko talabijin. Muddin ba su ruwaito wannan abu ba, karya ce.
 2. Idan labari ne da harshen Ingilishi, a kwafi wani bangaren labarin ko taken labarin, a je Google a bincika. Idan da gaske ne za a ga labarin an ruwaito shi. Hanya mafi sauki ma ita ce a je taskar labaran Google da ke: https://news.google.com ko daga wacce kasa ce aka buga labarin, muddin aka je wannan shafi, aka nemo ta hanyar rubuta taken, za a gani. In kuwa ba a gani ba, to labarin bogi ne.
 3. Akwai lambobin waya da hukumomi ke bayarwa, sannan akwai adireshin yanar sadarwa (web address) da dukkan hukumomin gwamnati suka mallaka. duk abin da aka ce wata hukuma ta yi ko za ta yi, na tallafi, idan ka je shafinta za ka gani.