✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Coronavirus: Za a kama direbobin da ke saba ka’ida a Abuja

Hukumar Gudanarwar Babban Birnin Tarayya a Najeriya ta bayar da umarni a kama duk wani direba da ya debi fasinjojin da suka haura adadin da…

Hukumar Gudanarwar Babban Birnin Tarayya a Najeriya ta bayar da umarni a kama duk wani direba da ya debi fasinjojin da suka haura adadin da ya kamata.

Shugaban Kwamitin Cika-Aiki na Ministan Abuja kan Tabbatar da Bin Dokokin Hanya ne ya bayyana haka ranar Lahadi.

A cewar Ikharo Attah, a wannan lokaci da duniya ke fafutukar hana cutar Coronavirus ko COVID-19 yaduwa ta hanyoyi daban-daban, ciki har da karfafa gwiwar mutane su rika yin nesa da juna (wato social distancing), bai kamata direbobi su rika makare motocinsu ba don kawai suna neman taro da sisi.

“Duk wanda aka kama ya dauki fasinja biyu a gaba, to za a kwace motar sannan a karbe lasisinshi na tuki”, inji Mista Attah.

Galibi direbobin kananan motocin haya a birnin Abuja kan debi fasinjoji hudu ne a kujerar baya a maimakon mutum uku na ka’ida, yayin da wadanda ke zirga-zirga a unguwannin da ke wajen birnin kan kara mutum guda a gaba—ma’ana suna daukar mutum uku ke nan duk da direba.

Mista Attah ya kara da cewa baya ga barazana ga lafiyar al’umma, hakan ka iya haddasa hadari saboda yana hana direba sauya giya cikin sauki.

Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN) ya kuma ambato shi yana kira ga masu motocin haya su sa ido sosai a kan fasinjojinsu, su kuma kai rahoton duk wanda suka ga ya nuna alamar kamuwa da cutar da ta shafi numfashi.