✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coutinho ya koma Aston Villa a matsayin dan wasan aro

Aston Villa tana da zabin kulla yarjejeniyar dindindin da dan wasan.

Tsohon dan wasan Liverpool, Phillippe Coutinho ya koma Aston Villa a matsayin dan wasan aro daga Barcelona zuwa karshen kakar wasanni ta bana.

Yarjejeniyar da Aston Villa ta kulla da dan wasan mai shekara 29 ta ta’allaka ne a kan gwajin lafiya da kuma samun izinin aiki a Birtaniya, inda ake sa ran zai garzaya garin Birmingham nan da awa 48 masu zuwa.

Bayanai sun ce Aston Villa tana da zabin kulla yarjejeniyar dindindin da dan wasan, inda a yanzu za ta rika biyan abin da bai kai kaso 50 cikin 100 na albashi da alawus-alawus da yake dauka duk mako.

Sky Sport ta ruwaito cewa, akwai yiwuwar za a samu kyakkyawar alaka tsakanin Coutinho da kocin Aston Villa, Steven Gerrard, la’akari da yadda suka shafe shekaru biyu da rabi tare a Liverpool.

A watan Janairun 2018 ne dan wasan na kasar Brazil ya koma Barcelona daga Liverpool a kan fan miliyan 146, sai dai fadi-tashin samun gindin a zamansa na Barcelona ya ci tura, inda ya shafe kakar wasanni ta 2019/2020 a matsayin dan wasan aro a Bayern Munich.

Haka zalika, rashin katabus da kuma tsammanin ba zai kawo wa Barcelona wani sauyi ba, ya sanya suke neman kai da shi.

Arsenal da Everton da Newcastle da kuma Tottenham na daga kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan.