✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coutinho ya zama dan wasan Aston Villa na dindindin

An zaftare albashin dan wasan da kusan fiye da kashi 70 cikin 100.

Philippe Coutinho ya zama dan wasan Aston Villa na dindindin bayan kungiyar ta biya Barcelona Yuro miliyan 20 a matsayin kudin sakar mata shi.

Dan wasan ya rattaba hannu kan kwantaragin kaka hudu a Aston Villa, inda ya amince a zaftare kusan fiye da kashi 70 cikin 100 na albashin da yake dauka a Barcelona.

Jaridar Telegraph ta ruwaito cewa Coutinho zai rika karbar albashin Fam 125,000 duk mako a Aston Villa.

Aston Villa ta dade da shiga jerin kungiyoyin Firimiyar Ingila da ke zawarcin Philippe Coutinho, bayan da dan wasan ya nuna yana son barin Nou Camp.

Tun a watan Janairun da ya gabata ne Philippe Coutinho ya koma Aston Villa a matsayin dan wasan aro daga Barcelona zuwa karshen kakar wasanni ta bana.

Yarjejeniyar da aka kulla a wancan lokaci ta kayyade cewa Aston Villa tana da zabin kulla yarjejeniyar dindindin da dan wasan, inda ta amince za ta rika biyan abin da bai kai kaso 50 cikin 100 na albashi da alawus-alawus da yake dauka duk mako.

Haka ita ma Barca ta dade tana fatan sayar da dan kwallon Brazil, mai shekara 29, bayan da ta dauki Ferran Torres daga Manchester City kan fam miliyan 55.

Shi ma Kocin Aston Villa, Steven Gerrard ya dade yana bayyana sha’awa salon taka ledar Coutinho, wanda suka buga kwallo tare a Liverpool.

A baya dai an rika alakanta Coutinho da sauran kungiyoyin da ke son daukar dan kwallon ciki har da Arsenal da Everton da Newcastle United da kuma Tottenham.

Coutinho na fatan komawa kan ganiya tun bayan da ya kasa taka rawa a Barcelona wadda ta dauke shi daga Liverpool kan fam miliyan 142.

Koda ya ke dan kwallon ya lashe Champions League a 2020 a Bayern Munich, wadda ta karba aro daga Barcelona, daga baya ya koma Camp Nou.

Coutinho ya taka rawar gani a Liverpool tare da Gerrard da suka yi tamaula da kadan ya rage kungiyar Anfield ta lashe Premier League a 2014

A halin yanzu dai Gerrard na ci gaba da neman hanyar da zai kara karfin Aston Villa tun bayan da ya maye gurbin Dean Smith daga Rangers a watan Nuwamba, inda a wancan lokacin ya ce ba zai yi gaggawar cefane ba.