✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Abdul Samad Rabiu ya ba da Naira biliyan 3.3

Hamshakin dan kasuwar nan dan asalin jihar Kano mai rukunin kamfanonin BUA, Alhaji Abdul Samad Rabiu, ya ce zai bayar da tallafin Naira biliyan uku…

Hamshakin dan kasuwar nan dan asalin jihar Kano mai rukunin kamfanonin BUA, Alhaji Abdul Samad Rabiu, ya ce zai bayar da tallafin Naira biliyan uku da miliyan 300 ga yakin da ake yi da cutar coronavirus, musamman a jihohin Kano da Legas.

Alhaji Abdul Samad ya bayyana haka ne a wata wasika da ya rubuta wa Kwamitin Cika Aiki na Shugaban Kasa a Kan Yaki da Cutar Coronavirus ranar Juma’a.

“Na damu matuka da yadda cutar coronavirus ke karuwa, musamman a jihohin Kano da Legas, duk da fafutukar da ake yi ba ji ba gani don yakar ta a Najeriya”, inji shugaban na BUA.

Ya kuma ce duk da kokarin Kwamitin na Shugaban Kasa da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) abin a yaba ne, kowa ya san akwai bukatar kara zage dantse.

Alkaluma na baya-bayan nan da hukumar ta NCDC ta fitar dai sun nuna cewa zuwa karfe 11.50 na daren 26 ga watan Afrilu, wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya sun kai 1,273.

Dan kasuwar ya nuna damuwa musamman game da yadda cutar ke yaduwa kamar wutar daji a Kano da kuma mace-macen da ake samu a ’yan kwanakin nan.

“Bisa la’akari da abin da ke faruwa yanzu haka a Kano mun yanke shawarar daukar matakin gaggawa na samar da tallafin Naira biliyan uku da miliyan 300 ga Kwamitin Shugaban Kasa da NCDC da sauran masu ruwa da tsaki don a samar da kayan aiki a cibiyoyi biyu na dindindin a jihohin Kano da Legas….

“Don haka ne, ba tare da bata lokaci ba, zan samar da tallafi biyu – ta hannun Gudauniyar BUA – na Naira biliyan biyu don agazawa Kano, da kuma Naira biliyan day aga jihar Legas kasancewar su ne suka fi yawan wadanda suka kamu a Najeriya.

“Sannan kuma za mu samar da tsabar kudi Naira miliyan 300 nan take ga Kwamitin Cika Aikin a Shugaban Kasa don taimaka masa wajen tsare-tsare da gudanar da ayyukansa”, inji Alhaji Abdul Samad.

Ya kuma ce zai bayar da kudin ne kari a kan abin da ya riga ya bayar ga wata gamayya ta ’yan kasuwa da ke tallafawa a yakin da CODID-19.

Dan kasuwar ya kara da cewa yana sa rai za a yi amfani da da wadannan kudade don samar da cibiyoyin cikin dan kankanin lokaci.

A baya ma dai Alhaji Abdul Samad Rabiu ya bayar da gudunmawar Naira biliyan daya don tallafawa a yunkurin da ake yin a kwao karshen annobar corona virus a Najeriya, sannan ya bayar da gudunmawar kayan aiki ciki har da kayan gwajin cutar da kayan kariya ga jihohi tara.

Wannan ce dai gudunmawa ta baya-bayan nan da kamfanoni da kungiyoyi da ma daidaikun mutane suka bayar don yaki da cutar coronavirus a Najeriya.