✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19: Abubuwa 7 da ya kamata Ku sani a kan rigakakin AstraZeneca

A ranar Juma’a ne Najeriya ta kaddamar da yin allurar rigakafin cutar COVID-19 ga ’yan kasa. Ko a ranar Asabar ma sai da aka yi…

A ranar Juma’a ne Najeriya ta kaddamar da yin allurar rigakafin cutar COVID-19 ga ’yan kasa.

Ko a ranar Asabar ma sai da aka yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo allurar rigakafin a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja.

An yi musu rigakafin ne dai nau’in AstraZeneca domin karfafa gwiwar miliyoyin ’yan Najeriya kan tabbacin sahihancinta da kuma tasirinta wajen yaki da cutar wacce ya zuwa yanzu ta hallaka miliyoyin mutane a fadin duniya.

Najeriya dai ta karbi rigakafin ta Oxford/AstraZeneca kusan miliyan hudu a ranar Talatar da ta gabata wacce aka kawo karkashin wani tsarin kasa da kasa.

Ga wasu muhimman abubuwa guda bakwai da ya kamata ku sani game da rigakafin:

  • Oxford AztraZeneca, kamar yadda sunan ke nuni Jami’ar Oxford dake Burtaniya ce ta sarrafa daga nau’in maganin wata kwayar cutar mura wacce ake kira adenovirus da ake samu a jikin birrai. An yi wa kwayar kwaskwarima domin ta yi maganin Coronavirus amma ta fuskar da ba za ta cutar ba.
  • Da zarar an yi wa mutum, allurar ta Oxford AztraZeneca za ta horar da garkuwar jikin dan Adam yadda za ta yaki Coronavirus. Ta haka, za ta takaita yaduwa cutar.
  • Sabanin rigakafin kamfanin Pfizer da dole a ajiye shi a wuri mai matukar sanyin da ya kai -70c, rigakafin Oxford za a iya ajiye shi a cikin kowanne irin firinji.
  • Ayarin mutanen da ya sarrafa rigakafin ya yi la’akari da bayanan da ya tattara daga gwaje-gwajen da aka yi a kasashen Brazil da Afrika ta Kudu da kuma Burtaniya.
  • Amfani da kwalba daya ta rigakafin na da tasirin kimanin kaso 76 cikin 100 na kare mutum daga COVID-19.
  • Gaggauta sake amfani da rigakafin a karo na biyu ba dole ba ne kuma ba zai yi matukar tasiri ga jiki ba.
  • Wasu masana garkuwar jikin dan Adam sun gargadi mutanen da aka yi wa rigakafin da kada su yi watsi da bayar da tazara, sanya takunkumi, tsaftace hannuwa da sauran matakan kariya daga cutar.