✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Adadin sabbin kamuwa na raguwa a Kano

Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) na baya-bayan nan sun nuna cewa adadin sabbin kamuwa ya ragu sosai a jihar Kano,…

Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) na baya-bayan nan sun nuna cewa adadin sabbin kamuwa ya ragu sosai a jihar Kano, inda aka samu karuwar mutum 14 a daren Laraba 13 ga watan Mayu.

A sanarwar da hukumar ta fitar a daren Talata da Laraba alkaluman sun nuna an samu raguwar sabbin kamuwa a kasa baki daya, inda yawan sabbin majinyatan ya gaza  mutum 200 a ko wanne daga cikin kwanakin biyu.

Kididdigar NCDC din ta tsakar daren 13 ga watan Mayu dai ta nuna cewa mutum 184 ne suka kamu, lamarin da ya kai jimillar wadanda aka tabbatar zuwa 4,971.

Hukumar ta NCDC ta kuma ce a cikin wannan adadi an rasa mutum 164; yayin da aka sallami 1,070 bayan sun warke.

Hakan dai na nufin a yanzu haka akwai mutum 3,901 da ke jinya.

Daga cikin sabbin majinyatan dai 51 a jihar Legas suke, 23 a Jigawa, 16 a Bauchi da Katsina,  14 a Kano, da kuma 10 a Rivers da  Yankin Babban Birnin Tarayya.

Sai kuma mutum tara a jihar Kwara, biyar a Delta da Kaduna, hudu a Sakkwato da Oyo, sai  Kebbi da Nasarawa da Osun da ke da mutum uku uku, da kuma  biyu a jihar Ondo.

Jihohin Ebonyi, Edo, Enugu, Anambra, Filato, da Neja na da mutum guda ko wacce.

Jihar Legas ce dai ke kan gaba a yawan wadanda aka tabbatar da mutum 2,041, sai Kano mai 707, sannan Yankin Babban Birnin Tarayya mai 370.