✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: An bayyana ranar sake bude makarantu a jihar Legas

Kwamishiniyar ilimin jihar ta ce za a sake bude makarantun a ranar 18 ga Janairun 2021.

Gwamnatin jihar Legas ta sanar da ranar 18 ga watan Janairun 2021 a matsayin ranar sake bude makarantun jihar don ci gaba da zangon karatu na 2020/2021.

Kwamishiniyar Ilimi ta jihar, Misis Folasade Adefisayo ce ta bayyana hakan ranar Litinin, inda ta ce za a sake bude su ne cikin matakan kariya da Gwamnatin Tarayya ta shimfida.

A watan Disambar 2020, gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya ba da umarnin sake rufe makarantun saboda sake bullar cutar COVID-19 a karo na biyu.

Kwamishiniyar ilimin ta kuma jaddada muhimmancin bin matakan kariya, don tafiyar da makarantun yadda ya dace.

Misis Folasade ta kuma shawarci makarantun kan yadda za su samar da tsarin yi wa dalibai bitar karatu daga gida, musamman ga wadanda ba su da lafiya ko wadanda suka kamu da COVID-19.

Sannan ta ce dole ne ga dalibai, malamai, masu ziyara su rika amfani da takunkumin rufe fuska, sannan a samar da wajen wanke hannuwa da kuma tabbatar da tsaftar makarantun.