✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: An samu karin samfurin Delta guda 10 a Najeriya —NCDC

NCDC ta ce alamomin cutar sun sha banban da wadanda aka saba gani.

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta ce an samu bullar sabuwar samfurin kwayar COVID-19 ta Delta a jikin kusan mutum 10 a Najeriya.

Babban Daraktan hukumar, Dokta Chikwe Ihekweazu ne ya bayyana hakan a Abuja lokacin da yake yi wa Ministan Lafiya karin bayani a kan inda aka kwana a yaki da cutar a ranar Litinin.

A cewarsa, “Kawo yanzu mun sami rahoton nau’in samfurin cutar har guda 10. Abin da muke yi shi ne gwajin matafiya da ke shigowa Najeriya. Yawancin wadanda aka samu da ita sun shigo ne ta Legas da Abuja.

“Alamominta sun sha bamban da na wacce muka saba gani, dalilin ke nan da muke bukatar mu kara lura sosai,” inji shi.

Ihekweazu, wanda ya sami wakilcin Daraktan Sashen Sa’ido a kan Cututtuka na Hukumar ya ce yawan masu kamuwa da cutar ya karu da kaso 24 cikin 100, idan aka kwatanta da alkaluman da aka rika samu a ’yan makonnin baya.

Ya ce ya zuwa 22 ga watan Yulin 2021, Najeriya ta tabbatar da kamuwar mutum 22,130 da cutar Kwalara, yayin da 526 daga ciki suka mutu a cikin jihohi 18 da Babban Birnin Tarayya Abuja.

Da yake jawabi, Ministan Lafiya, Dokta Osagie Ehanire ya ce duniya ta fuskanci karuwar masu kamuwa da cutar a kasashe cikin sa’a 24 da suka gabata sakamakon yaduwar nau’in cutar na Delta.

Ya ce babbar barazanar a yanzu ba ta wuce ta shigo wa Najeriya da cutar daga kasashen da aka fi zuwa daga kasar ba irin su Burtaniya da Amurka da Hadaddiyar Daular Larabawa da Faransa da kuma Turkiyya.

Ministan ya ce lamarin abin damuwa ne matuka kasancewar cutar ta sake bulla a karo na uku, amma duk da haka jama’a na ci gaba da nuna halin halin ko-in-kula da matakan kariyar da ma’aikatan lafiya suke bayarwa.