✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: An sake sanya dokar kulle a Anambra

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne don dakile yaduwar cutar a tsakanin mutanen jihar.

Gwamnatin Jihar Anambra ta da dawo da dokar hana fita a jihar, wadda za ta fara aiki daga ranar Litinin 8 ga Fabrairu 2021.

Sanarwar na kunshe ne cikin wani jawabi da Sakataren Gwamnatin Jihar,  Solo Chukwulobelu, ya sanya wa hannu a ranar Juma’a.

“Gwamna Willie Obiano ya umarci ma’aikata daga mataki na 12 zuwa kasa da su ci gaba da aiki daga gida.

“Gwamnatin jihar nan na ci gaba da tabbatar da mutane na bin matakan kariyar COVID-19.

“Gwamnati ta kafa kotun tafi-da-gidanka, a fadin jihar don hukunta masu karya dokokin cutar coronavirus da aka shimfida,” inji Chukwulobelu.

Sai dai a wannan karon, Sakataren Gwamnatin jihar ya ce dokar kullen za ta fara aiki ne daga karfe 9 na dare zuwa karfe 6 na safe, a kullum.

Sannan an kafa kwamitin hadin gwiwa daga Ma’aikatar Lafiya da Ma’aikatar Kasuwanci, don zagawa cikin kasuwanni tare da sanya ido kan yadda jama’a za su ke bin matakan kariyar cutar.