✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19: An sallami mutum 20 a Gombe

Gwamnatin jihar Gombe ta sallami mutum 20 da aka killace aka yi musu jinya sakamakon kamuwa da cutar coronavirus. An sallami mutanen ne bayan an…

Gwamnatin jihar Gombe ta sallami mutum 20 da aka killace aka yi musu jinya sakamakon kamuwa da cutar coronavirus.

An sallami mutanen ne bayan an yi musu gwaji har sau biyu an ga ba sauran cutar a tare da su.

Da yake bayani ga manema labarai kafin sallamar majinyatan, Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Ahmed Muhammad Gana, ya ce mutanen 20 na cikin mutum 103 da aka tabbatar suna dauke da cutar kuma za a sallami 10 daga Asibitin Cututtuka Masu Yaduwa na Farfesa Idris Muhammad da ke garin Kwadom a yankin karamar hukumar Yamaltu Deba da kuma wasu 10 dake Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya (FTH) da ke Gombe.

Kwamishinan, wanda ya yi bayanin a madadin shugaban kwamitin yaki da cutar, ya nemi hadin kan yan jarida a jihar wajen yada labarai masu inganci kan wannan cutar ba tare da yada labarin da zai jawo tashin hankali ba.

Ya kuma bukaci al’ummar gari su ma su bai wa yan kwamitin hadin kai don yaki da cutar.

Daga nan ya ce ganin cewa wadanda aka killace din su ke daukar dawainiyar iyalan su kuma sun yi korafi a kan halin da iyalan nasu ke ciki, gwamnatin jihar Gombe za ta taimaka musu a tsarinta na ba da tallafi.

Da yake karin haske, Kwamishina  Ilimi na jihar, Dokta Habu Dahiru,  kira ya yi ga jama’a da cewa kada su kyamaci wadanda aka sallama a lokacin da suka shiga cikin su.

Dokta Dahiru ya kuma ce kafin a sallami wadannan mutane sai da aka yi musu gwaji sau biyu aka tabbatar ba su dauke da wanann cutar.

Tun da farko dai da safiyar Juma’a masu dauke da cutar da ke FTH sun yi zanga-zanga kamar yadda wadanda suke garin Kwadom suka yi ranar Talatar da ta gabata inda suke zargin an yi watsi da su kuma an ki a sallame su bayan sun share sama da makonni biyu a killace.