✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: A bar mutum 12 su yi sallar Juma’a —Shaikh Dahiru Bauchi

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma masanin Tafsiri, Shaikh Dahiru Usman Bauchi, ya ce bai kamata a hana sallar Juma’a da ta Tarawihi ba a…

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma masanin Tafsiri, Shaikh Dahiru Usman Bauchi, ya ce bai kamata a hana sallar Juma’a da ta Tarawihi ba a cikin watan Ramadana.

Shaihun malamin ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai ranar Laraba.

“Tun da taruwar jama’a da yawa ake gudu, ya kamata a ko wanne masallacin Juma’a akalla a samu mutum 12 su yi sallah.

“Ita ma sallar Tahajjudi da sallar Asham kada a daina, a ko wanne masallaci a samu ko da mutum bakwai su dinga yin sallah tun da hukumomin lafiya sun ce kada a wuce mutum 50, su ma kada su cudanya da juna—sai a yi yadda aka ce ba tare da cunkoson ba, amma kada a daina sallah a masallaci”, inji Shaikh Dahiru Bauchi.

Shaikh Dahiru Bauchi ya kuma ce bisa la’akari da halin da ake ciki, a Bauchi zai yi Tafsiri bana, ba a Kaduna ba.

“In Allah Ya yarda a bana za a gudanar da Tafsiri ne a Bauchi, ba sai an je Kaduna ba, kuma za a turo ’yan jarida daga Kaduna da sauran wurare daban-daban domin su dauki Tafsirin a watsa a duniya”, inji shaihun malamin.

Ya kuma shawarci al’ummar Musulmi da a dage da addu’a—a karanta Fatiha kafa daya, Istigfari 4444, Salatul Fatihi 4444, Hailala 4444, da aya ta 12 a Suratul Dukhan kafa 4444.

Annobar cutar coronavirus dai ta haddasa ayyana dokar hana fita a jihohin Najeriya da dama, da dakatar da sallar Juma’a da ma tarukan al’ada da na ibada.

Za a iya karanta cikakken bayani a jaridar Aminiya ta Juma’a 17 ga watan Afrilu, 2020.