✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Buhari, Monguno da Ministoci 2 sun killace kansu

Za su yi hakan ne domin bin umarnin NCDC.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ’yan tawagarsa yayin tafiyarsa zuwa Landan za su killace kansu kamar yadda matakan kariyar COVID-19 suka tanada.

Kakakin shugaban, Malam Garba Shehu ne ya tabbatar da hakan ga Aminiya ranar Lahadi, inda ya ce daukar matakin ya zama wajibi bayan Najeriya ta rufe ofishin jakadancinta na tsawon kwanaki 10 a can, don bin ka’idojin Burtaniya kan yaki da cutar.

An dai kulle ofishin ne bayan rahotanni sun nuna wasu daga ma’aikatan cikinsa sun kamu da cutar, ciki har da Jakadan Najeriya a can, Ambasada Sarafa Tunji Isola, wanda aka gani dab da Buharin a filin jirgin saman Landan.

Shugaba Buhari dai ya dawo Najeriya ne ranar Juma’a, 13 ga watan Agustan 2021 bayan ya shafe kwana 18 a Landan.

Ya kuma hadu da jagoran APC na Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a birnin na Landan, ana jajiberin dawowar tasa.

Buhari dai ya je Burtaniyar ne domin halartar wani taro kan ilimi, kafin daga bisani kuma ya wuce ya gana da likitocinsa.

Daga cikin wadanda suka raka shi akwai Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, da Minista a Ma’aikatar Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba da mai ba shugaban shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno da kuma Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Najeriya (NIA), Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar.

Sai dai Garba Shehu ya tabbatar da cewa Shugaban da dukkan ’yan tawagar tasa za su killace kansu

Ya ce, “Mai girma Shugaban Kasa da duk ’yan tawagarsa za su killace kansu kamar yadda NCDC ta ba da shawara ga duk wanda ya yi tafiya zuwa wata kasar.

“Dukkansu an gwada su ranar Juma’a, kuma za a sake yi musu wani gwajin nan ba da jimawa ba,” inji Malam Garba Shehu.