✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Buhari ya ce a biya malaman jami’a

Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umarni a biya malaman da ke karantarwa a jami’o’in gwamnatin tarayya albashinsu na watannin Fabrairu da Maris da aka…

Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umarni a biya malaman da ke karantarwa a jami’o’in gwamnatin tarayya albashinsu na watannin Fabrairu da Maris da aka rike saboda ba su yi rajista da sabon tsarin biyan albashi na IPPIS ba.

Minsitan Kwadago da Samar da Ayyukan-yi Chris Ngige ne ya bayyana haka a wata sanarwa da mai taimaka mishi a bangaren kafofin sadarwa na zamani, Emmanuel Nzomiwu, ya sanyawa hannu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito ministan yana cewa shugaban kasar ya kuma umarci ministar kudi da akanta janar na tarayya su tabbatar an biya albashin cikin gaggawa don ya rage wa malaman da iyalansu radadin matakan da suka biyo bayan barkewar annobar COVID-19.

Ngige ya kuma kara da cewa an bukaci shugabannin jami’o’in da su mika lambobin tabbatar da sahihancin asusun ajiya (BVN) na malaman ga akanta janar na tarayya.

Idan ba a manta ba, gwamnatin tarayya ta umarci dukkan makarantunta na gaba da sakandire su shiga sabon tsarin na IPPIS daga watan Fabrairu, lamarin da ya jawo takaddama tsakanin malamai da hukumomi.