✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID 19: Gwamnan Sakkwato yana rokon addu’a

Tambuwal na killace bayan manyan mutane da ya ziyarta sun kamu da COVID-19

Gwamnan Sakkwato, Aminu Tambuwal ya killace kansa bayan tafiye-tafiyen da ya yi a kwanakin baya domin ya ganawa da manyan mutane da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19.

Bayan sakamakon gwaji ya nuna mutanen da gwamnan ya ziyarta sun kamu da cutar, sai masana suka ba shi shawarar ya killace kansa.

“Kan haka na janye duk wata mu’amala ta aiki a zahiri har sai na kammala sharuddan da aka gidanya kan cutar COVID-19 daga yau Jumu’a,” ini shi.

Tambuwal a wata takarda da ya fitar aka raba wa manema labarai ya ce ya mika ragamar jagorancin jihar ga mataimakinsa, Manir Muhammad Dan’iya kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Ya ce zai bi sharuddan kwamitin kula da cutar na Jihar Sakkwato da Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa, (NCDC) da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO); zai bari a yi masa gwaji kuma a fitar da sakamakon don jama’a su sani.

Haka ma ya yi kira ga jama’ar Jihar Sakkwato su bi dokokin kariyar cutar, a yawaita yi masa addu’a a wannan yanayi, Allah Ya yi wa mutanen Sakkwato da Najeriya albarka.