✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Gwamnatin Taraba ta yi gargadi kan bukukuwa

Ta ce a kaurace wa taruka sannan a rika sanya takunkumi

Gwamnatin Taraba ta gargadi jama’arta kan barazanar yaduwar cutar coronavirus sakamakon karya dokar kariyar cutar a jihar.

Kwamishinan Lafiyar Jihar, Dokta Innocent Vakkai ya yi gargadin ne a ranar Litinin lokacin da yake bayani kan yiyuwar dawowar cutar a karo na biyu, inda yace cutar tana da saurin yaduwa kamar wutar daji.

Dokta Vakkai, ya bayyana cewa akwai alamun yaduwar COVID-19 a jihar sakamakon kin bin dokokin hana yaduwarta da mutane ke yi.

Ya shawarci al’ummar Jihar da su kiyayi cudanya da mutanen da suka dawo daga kasashen waje a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.

Gargadin ya kuma bukaci su kaurace wa wuraren taruwar jama’a sannan a sanya takunkumi yayin da fitowa daga gidajensu a yayin bukukuwan na karshen shekara.

Ya bayyana cewa yanzu haka ana zargin masu yi wa kasa hidima (NYSC) 11 a jihar sun kamu da COVID-19 inda aka killace su ana jiran sakamakon gwajin cutar.

Ya ce an killace ne a Otel ne saboda yanzu haka babu cibiyar cutar da ke aiki sakamakon lalatawa da sace kayayyakin aikin da ke cibiyoyin da masu zanga-zangar ENDSARS suka yi.

“Duk da cewa ba mu samu rahoton mutuwar ko mutun guda da coronavirus ta kashe a jihar yayin bayyanarta karon farko ba, hakan ba ya nuna kar a kiyaye matakan dakile yaduwar cutar”, inji shi.