✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Gwamnatin Tarayya ta karyata sake sanya dokar kulle

Jagoran Kwamitin PTF ya ce jama'a su yi watsi da labarin.

Gwamnatin tarayya ta musanta labaran da ke yawo na cewa ta sake dawo da dokar kulle a fadin tarayyar kasar nan domin dakile bullar Coronavirus a karo na biyu.

Jagoran kwamitin Shugaban Kasa kan yaki da COVID-19, Dokta Sani Aliyu ne ya bayyana haka a cikin wani  bidiyo da ya yi a ranar Alhamis.

Dokta Sani Aliyu ya ce, “Muna sane da wani sako da ke yawo a kafafen sada zumunta cewar an dawo da dokar kulle, wannan ba gaskiya ba ne kuma ya kamata jama’a su yi watsi da shi.

“Ina rokon jama’a da su ci gaba da bin matakan kariyar COVID-19, ta hanyar amfani da takunkumi, rage shiga cunkoso da kuma wanke hannu.

“Muna da hanyoyin watsa labaranmu in har bukatar hakan ta sake tasowa; don haka a yi watsi da wancan sako da ke yawo a WhatsApp don ba gaskiya ba ne,” inji shi.

Ana iya tunawa Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta sanar a ranar Alhamis cewa a ranar Litinin 18 ga watan Janairun da muke ciki za a bude makarantu.

Hukumomin Najeriya na ci gaba da nuna damuwa kan yadda ‘yan kasar ke sabo dokokin kariyar cutar COVID-19 wadda yaduwarta a zagaye na biyu ya tashi hankalin kasashen duniya.

Zuwa yanzu dai sama da mutum 100,000 aka tabbatar da sun kamu da cutar a Najeriya, inda ta yi ajalin da dama daga cikin wadanda suka harbu da ita.