✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Kotun tafi-da-gidanka ta fara aiki a Kafanchan

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa Kotun tafi-da-gidanka a garin Kafanchan da ke karamar hukumar Jama’a don hukunta duk wanda ta kama da laifin saba dokar…

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa Kotun tafi-da-gidanka a garin Kafanchan da ke karamar hukumar Jama’a don hukunta duk wanda ta kama da laifin saba dokar zirga-zirga da aka sanya don dakile yaduwar cutar coronavirus.

Yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da kotun, Babban Sakatare a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kaduna, Mista Christopher Umar, ya bukaci kotun tafi-da-gidanka da ta gudanar da aikinta ba sani ba sabo don hukunta duk wanda ya taka dokar.

Umar ya kuma shawarci jama’ar yankin da su kiyaye dokar hana zirga-zirga da gwamnati ta sanya da sauran shawarwarin kiwon lafiya don tsare lafiya da rayukan al’umma gaba daya.

Ya ce daga cikin aikin kotun har da hukunta direbobin dake karya doka ta hanyar zirga-zirgar da ba ta cikin wadanda aka yarje a lokacin zaman gidan.

Yayin da yake tofa albarkacin bakinsa, shugaban karamar hukumar Jama’a, Peter Danjuma Averik, ya ce babu tantama samuwar kotun zai taimaka wajen sanya jama’ar yankin ci gaba da kiyaye dokar hana zirga-zirgar.

Averik ya kuma yi kira ga mutanen karamar hukumar da su bayar da hadin kai ga gwamnatin jihar a kokarinta na yaki da bazuwar cutar ta Covid-19 a fadin jihar.

Alqalin Kotun Majistiri na garin Kafanchan, Abdulaziz Ibrahim ne zai shugabanci kotun na tafi da gidanka.