✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Majinyata kusan 100 sun warke cikin kwana biyu a Legas

Ma’aikatar lafiya ta jihar Legas ta ba da sanarwar karin majinyata 37 da suka warke daga coronavirus. Sanarwar da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na…

Ma’aikatar lafiya ta jihar Legas ta ba da sanarwar karin majinyata 37 da suka warke daga coronavirus.

Sanarwar da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na Twitter da yammacin Laraba  ta ce 19 daga cikin majinyatan da suka warke mata ne, sai maza 18 da kuma dan kasar Indiya mutum guda.

Biyar daga cikin majinyatan an sallame su ne daga asibitin kula da masu dauke da  cututtuka masu yaduwa ta Yaba, sai 25 daga cibiyar killace masu cutar ta Onikan, da  kuma bakwai daga cibiyar da ke Eti-Osa.

Majinyata 97 suka warke aka kuma sallame su cikin kasa da kwanaki biyu a Legas, domin asanarwar da gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu, ya fitar a ranar Talata, 5 ga watan Mayu.

Ya shaida cewa majinyata 60 sun warke, maza 40, mata 20, wadanda aka sallama suka  koma cikin iyalansu.

Kawo yanzu majinyata 358 suka warke aka kuma sallame su a Legas, jihar da ke kan gaba a yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar.