✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Mutum 1 ya mutu wani ya kwanta magashiyyan bayan karbar rigakafi a Denmark

Tarayyar Turai dai ta ce ta gamsu cewa amfanin rigakafin ya zarce illarsa duk kuwa da wadannan matsalolin.

Kasar Denmark ta ce akalla mutum daya ya mutu ranar Asabar, wani kuma na can kwance rai kwakwai, mutu kwakwai bayan an yi musu rigakafin cutar COVID-19 samfurin AstraZeneca.

Mutum biyun wadanda dukkansu ma’aikatan lafiya ne dai sun kama rashin lafiyar ne kasa da makonni biyu bayan yi musu rigakafin, kamar yadda hukumomin asibitin dake birnin Copenhagen suka tabbatar.

Hukumar Kula da Lafiya ta Kasar dai ta tabbatar da cewa ta sami rahoton akalla korafe-korafen rashin lafiya guda biyu, ko da yake bat a yi cikakken bayani ba.

Kasar Denmark dai wacce ta dakatar da amfani da rigakafin na AstraZeneca ranar 11 ga watan Maris ta bi sahun kusan kasashe da dama wajen dakatar da amfani da maganin har sai masana kimiyya sun kammala bincike don gano ko akwai alaka tsakanin taruwar jinin da ake samu da rigakafin.

Sai dai wasu kasashen ciki har da Jamus da Faransa a cikin makon nan sun jingine dakatarwar da suka yi wa maganin bayan wani binciken da Tarayyar Turai ta gudanar a kan batun taruwar jinin.

Tarayyar ta Turai dai ta ce ta gamsu cewa amfanin rigakafin ya zarce illarsa duk kuwa da wadannan matsalolin.

To sai dai kasashen Denmark da Norway a ranar Juma’a sun ce suna bukatar lokaci kafin su yanke shawarar ko su ci gaba da amfani da rigakafin ko kuma a’a.

Kazalika, Daraktan Hukumar Kula da Magunguna (EMA) Emer Cooke ya ce sakamakon binciken da suka gudanar a kan sama da mutane 30 ya nuna cewa ba za a iya raba dangantaka tsakanin taruwar jinin da rigakafin ba.