✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Saudiyya ta ba da izinin kwashe ’yan kasashen waje

Ta amince jiragen kasashen su shigo su kwashe ’yan kasashensu da suka makale a kasarta.

Gwamnatin Saudiyya ta ba wa jirage daga kasashen waje izinin su shigowa su kwashe ’yan kasashensu da suka makale a kasarta.

Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta Saudiyya ta ce izinin bai shafi jirage daga kasashen da ke fama da sabon nau’in cutar COVID-19 da aka gano ba.

Kazalika ba a amince wa ma’aikata jiragen sama da suka sauka a Saudiyya  su fito daga jirgen ba.

Saudiyya ta rufe sufurin jiragen sama gaba daya na tsawon mako guda ne a makon jiya saboda rashin samun bayani kan sabon nau’in na COVID-19.

Kasar ta yi hakan ne bayan Gwamnatin Birtaniiya ta saka dokar hana fita a birnin London da yankin Kudu maso Gabashin Ingila don dakile cutar mai saurin bazuwa.