✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Saudiyya ta dakatar da ’yan kasashe 20 shiga kasarta

Ta hana baki daga Amurka, Ingila da Daurlar Larabawa da sauransu shigar ta saboda COVID-19.

Saudiyya ta dakatar da mutane daga wasu kasashe 20 shiga kasarta, a sabon yunkurinta na hana yaduwar cutar COVID-19 a karo na biyu.

Sanarwar daga Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Saudiyya ta ce umarnin Masarautar zai fara aiki ne daga ranar Laraba da dare.

“Matakin da aka dauka kan kasashe 20 din ya biyo bayan umarnin da Masarautar ta bayar.

“Duk dan kasar Saudiyya da ya fito daga kasashen zai shigo Saudiyya ne bisa matakan kariyar COVID-19,” inji sanarwar.

Rahotanni sun bayyana cewa jerin kasashen da Saudiyya ta dakatar din su ne: Amurka, Ingila, Jamus, Faransa, Turkiyya, Japan, Indiya, Pakistan, da Sweden.

Sauran su ne: Ajantina, Daular Larabawa, Indonisiya, Ireland, Brazil, Portugal, Afrika ta Kudu, Switzerland, Lebanon, Masar.