✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19 ta hana Ronaldo buga wasan Juventus da Barcelona

Sakamakon gwajin cutar COVID-19 na dan wasan Juventus, Cristiano Ronaldo ya fito, wanda ya nuna cewa har yanzu

Sakamakon gwajin cutar COVID-19 na dan wasan Juventus, Cristiano Ronaldo ya fito, wanda ya nuna cewa har yanzu yana dauke da cutar.

Hakan dai na nufin Ronaldo ba zai buga wasan Juventus da Barcelona ba.

Wasan dai shine wanda masoya kwallon kafa suka yi tsammanin za a sake kece raini tsakanin Ronaldo da tsohon abokin hamayyarsa, Lionel Messi a wasan gasar Zakarun Turai.

Idan ba a manta ba, Ronaldo ya kamu da cutar ne a lokacin da yake wakiltar kasarsa Portugal, inda zuwa yanzu ya rasa buga wasanni uku: daya da Portugal, biyu da Juventus.

An ta jiran sakamakon gwajin cutar na biyu, inda magoya bayan Juventus da masoyan dan wasan mai shekara 35 suka yi fatan zai samu sauki domin ya samu buga wasan.