✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19 ta kama sama da mutum 100,000 a Faransa ranar Kirsimeti

Adadin dai shi ne mafi girma da aka taba samu tun farkon barkewar cutar a kasar.

Kasar Faransa ta sanar cewa akalla mutum 104,611 ne suka kamu da cutar COVID-19 ranar Asabar, adadi mafi girma da aka taba samu a kasar tun farkon barkewar annobar.

Alkaluman na ranar Kirsimeti su ne karo na uku a jere da ake samun adadi mai yawa na mutanen da suke kamuwa da cutar a kasar.

Hakan na zuwa ne gabanin wani taro da Shugaban Kasar, Emmanuel Macron zai yi da kusoshin gwamnatinsa ranar Litinin kan matakan takaita ci gaba da yaduwar cutar.

Hukumomi dai na ci gaba da nuna damuwa kan yadda samfurin cutar na Omicron ke ci gaba da yaduwa kamar wutar daji.

Tuni dai hukumomin lafiya a ranar Juma’a suka ba da shawarar cewa ya kamata a sake yi wa tsofaffi rigakafin cutar wata uku bayan yi musu na farko.

A yanzu kuma gwamnati na duba yiwuwar tilasta nuna shaidar karbar rigakafin kafin mutum ya shiga muhimman wuraren taruwar jama’a a kasar da kuma tafiye-tafiyen kasa da kasa.

Tun farkon barkewar cutar dai, akalla mutum 122,546 ne suka mutu a kasar sanadiyyar cutar.

Ya zuwa yanzu kuma, an yi wa kusan kaso 76.5 cikin 100 na al’ummar kasar allurar rigakafin cutar.