✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19 ta kashe Janar din Sojin Najeriya

Janar din sojan Najeriya da ya kamu da COVID-19 ya kwanta dama

Babban Kwamandan Runduna ta 6 ta Sojin Kasa ta Najeriya da ke Fatakwal, Jihar Ribas Manjo Janar Olu Irefin ya kwanta dama.

Janar din sojan din ya rasu ne sakamakon kamuwa da cutar COVID-19.

Janar Olu Irefin, na daga cikin manyan jagorori a rundunar da ke halartar babban taron Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya na 2020 lokacin da aka gano ya kamu da cutar.

A safiyar Alhamis runduanr ta sanar da soke abubuwan da suka yi saura a taron da aka fara gudanarwa ranar Litinin.

Rundunar ta kuma umarci a killace ddukkannmin mahalarta taron na tsawon kwana 14 tare da kiyaye sauran matakan kariyan COVID-19.

Kafin zamansa Babban Kwamandan Runduna ta 6 da ke Fatakwal a watan Yuli, Janar Janar Olu Irefin shi ne Babban Kwamandan Runduna ta 81 da ke Legas.