✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19 ta kashe mutane 193 cikin kwanaki 20 a Najeriya

Ya zuwa ranar Laraba, akalla mutane 126,160 suka kamu da cutar a Najeriya, 1,544 kuma suka mutu.

Cutar Coronavirus na ci gaba da barna ta hanyar karuwar yawan masu dauke da ita da kuma wadanda take kashewa tun farkon sabuwar shekarar 2020 kamar yadda binciken Aminiya ya gano.

Alkaluman da muka tattara daga Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NCDC) sun nuna cewa mutane 193 ne suka mutu sanadiyyar cutar daga cikin kwanaki 20, tsakanin hudu da kuma 24 ga watan Janairun 2021.

Ya zuwa ranar Laraba, akalla mutane 126,160 aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya, 24, 251 daga cikinsu har yanzu suna dauke da ita, yayin da 1,544 kuma suka mutu.

Kazalika, a daidai lokacin da kasar Ya zuwa ranar Laraba, akalla mutane 126,160 aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya, 24, 251 daga cikinsu har yanzu suna dauke da ita, yayin da 1,544 kuma suka mutu.ta shiga zango na biyu na cutar a watan Nuwamban bara, yawaitar karuwar mace-mace daga cikin masu cutar na ci gaba da tayar da hankula matuka.

Za a daure masu karya matakan kariya watanni shida

Ko a ranar Larabar da ta gabata sai da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan wata doka da aka yi wa lakabi da ‘Kundin Dokokin Kariyar COVID-19 na 2020’, domin tabbatar da ana bin matakan kariya daga cutar.

Dokar dai ta yi tanadin hukuncin daurin watanni shida ga dukkan wanda aka samu ya karya dokokin da ta tanada.

Sabon nau’in cutar ya bulla a Najeriya

Bugu da kari, Gwamnatin Tarayya a ranar Litinin ta kuma tabbatar da cewa sabon nau’in cutar wanda ake wa lakabi da B117 da aka samo daga kasar Burtaniya ya bulla a Najeriya.

Da yake jawabi yayin taron Kwamitin Kar-ta-kwana da Gwamnatin Tarayya ta Kafa don Yaki da Cutar kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya ce masana ilimin kimiyya sun dukufa wajen nazarin cutar.

Ya kuma koka kan yadda ya ce ana kara samun masu dauke da cutar a cikin ’yan makonnin nan, musamman ta la’akari da rahoton alkaluman da suke fita a kullum.

Tsakanin ranakun Alhamis 21, da Laraba 27 ga watan Janairun 2021 kawai, kimani mutane 11,469 ne suka kamu da cutar, 59 daga ciki kuma suka mutu.