✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19 ta kashe mutum 44 cikin shekara 1 a Gombe

Kwamitin Yaki da cutar Corona a jihar Gombe ya ce an sami asarar rayukan mutane 44 a fadin jihar tun bayan bullar cutar a bara.

Kwamitin Yaki da cutar Corona a jihar Gombe ya ce an sami asarar rayukan mutane 44 a fadin jihar tun bayan bullar cutar a bara.

Adadin dai na daga cikin mutum 34,472 da aka sami nasarar gwadawa, cikinsu aka sami 234 dauke da cutar sannan aka sallami 1,990 bayan sun warke daga cibiyoyin killace masu cutar.

Shugaban Kwamitin Yaki da Cutar a Jihar, kuma Mataimakin Gwamnan jihar Manasseh Daniel Jatau ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida kan cikar kwamitin shekara daya da kafuwa.

Jatau ya ce ranar 20 ga watan Afirilu 2021 ne kwamitin ya cika shekara guda cif da kafuwa.

A cewarsa, jihar Gombe ta sami gagarumar nasara cikin shekara daya, inda ta gina asibitoci da samar musu da kayan aiki guda 12, ta gina babban dakin gwajin cutar a Asibitin Kwararru na jihar.

Bugu da kari, ya ce jihar ta samar da motoci kirar Hilux guda 11 sannan rarraba kayan tallafin abinci a mazabu 2,218 dake jihar.

A bangaren Rigakafin cutar kuwa ya ce yanzu haka jihar ta sami nasarar yi wa kimanin mutane dubu  32,956 allurar a zagayen farko.

Daga nan sai Mataimakin Gwamnan ya gargadi al’umma cewa har yanzu akwai cutar don haka yana da kyau a kiyaye dokokinta wajen yawaita wanke hannu da ba da tazara a tsakanin.