✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19 ta sake kama mutum 1,547 a Najeriya — NCDC

Mutum 1,547 ne suka sake kamuwa da COVID-19 a Najeriya.

Mutum 1,547 ne suka sake kamuwa da cutar COVID-19 a Najeriya ranar Lahadi, kamar yadda Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta sanar.

Tun farkon bullar cutar a watan Fabrairun 2020 dai, jimlar wanda suka kamu da ita a Najeriya ya kai 237,561.

Kawo yanzu, kwayar cutar ta yi ajalin mutum 3,022 a fadin Najeriya.

An sallami adadin mutum 212,550 na wanda suka kamu, 193 kuma a ranar Lahadi aka sallame su.

NCDC a ranar Litinin ta sanar da jihohi tara inda aka samu adadin wanda suka kamu a ranar ta Lahadin da ta gabata.

Babban Birnin Tarayya Abuja ne ke kan gaba da mutum 806, yayin da Jihar Legas ke biye mata baya da 401.

Jihar Borno na da 166, Oyo 78, Ogun 47, Osun 30, Ekiti da Katsina na da bakwai-bakwai kowanensu.

Jihar Kano na da mutum hudu da suka harbu, Jigawa kuma na da mutum daya.

An yi wa adadin mutum 3,751,696 gwajin COVID-19 tun bayan bullarta a Najeriya.