✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19 ta sake kashe ministoci 2 a Zimbabwe

Ministoci biyu masu ci a kasar Zimbabwe sun sake mutuwa bayan kamuwa da cutar COVID-19, lamarin da ya sa kasar ta sanar

Ministoci biyu masu ci a kasar Zimbabwe sun sake mutuwa bayan kamuwa da cutar COVID-19, lamarin da ya sa kasar ta sanar da shirye-shiryen sake kakaba dokar kulle domin dakile ci gaba da yaduwar cutar.

Da yammacin ranar Juma’a ne dai gwamnatin kasar ta sake sanar da rasuwar Ministan Sufurin kasar, Joel Matiza, kasa da kwanaki biyu bayan Ministan Harkokin Wajen Kasar, Sibusiso Moyo shima ya rasu sanadiyyar cutar.

Ya zuwa yanzu dai karin ministoci biyu ne suka sake kamuwa da cutar a kasar.

Wasu rahotanni dai da ba a kai ga tantancewa ba sun ce wasu ministocin guda hudu kuma yanzu haka na can suna fadi tashin neman maganin cutar a asibitoci masu zaman kansu.

“Mun shiga wani mawuyacin hali da ba mu san yadda za mu fita daga cikinsa ba,” inji Mataimakin Ministan Lafiyar kasar, John Mangwiro, a hirarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na DPA.

John ya kuma ce kasar na shirye-shiryen sake dawo da dokar kulle wacce aka sake dawo da ita tun farkon watan Janairu.

Kazalika, an tilastawa wuraren sayar da abinci, na motsa jiki da na shaye-shaye su rufewa.

’Yan kasar da dama dai sun bazama kafafen sada zumunta na zamani inda suka rika zargin Shugaban Kasar, Emmerson Mnangagwa da wanda ya gaje shi, marigayi Robert Mugabe kan mawuyacin halin da harkar lafiyar kasar ta tsinci kanta a ciki.

Yanzu haka dai ma’aikatan lafiyar kasar suna yajin aiki saboda abinda suka kira karancin kayan kariya daga cutar da kuma kin biyansu albashi da kuma sauran hakkokinsu.

Mutane 30,532 ne suka kamu da cutar a kasar tun bayan barkewarta a 2020, yayin da 962 kuma suka mutu.