✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

COVID-19: Tsohon gwamnan jihohin Kano da Binuwai ya rasu

Ya kuma taba tsayawa takarar gwamnan jihar Neja a karkashin jam’iyyar ta PDP 2015.

Tsohon gwamnan mulkin soja a jihohin Kano da Binuwai, Kanal Aminu Isah Kontagora (mai ritaya) ya rasu.

Marigayin, wanda kuma jigo ne a jam’iyyar PDP ta jihar Neja ya rasu ne da sanyin safiyar Litinin a wani asibiti a Abuja bayan fama da cutar COVID-19.

Ya rasu yana da shekaru 65 a duniya.

Kanal Aminu ya kuma taba tsayawa takarar gwamnan jihar Neja a karkashin jam’iyyar ta PDP a zaben shekara ta 2015.

Marigayin dai ya zama gwamnan mulkin soja na jihar Binuwai daga shekarar 1996 zuwa 1998, zamanin mulkin tsohon Shugaban Kasa, marigayi Janar Sani Abacha.

Kazalika, Kontagora ya zama gwamnan jihar Kano daga watan Satumban 1998 zuwa watan Mayu na 1999 inda ya mika ragamar mulkin jihar ga sabon zababben gwamnan farar hula a jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso.