✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Yadda doka ta shafi masu kayan abinci a Abuja

A ka’idar dokar da ta hana fita ko bude shaguna da sauran wuraren harkoki na yau da kullum a Yankin Babban Birnin Tarayyar Najeriya da…

A ka’idar dokar da ta hana fita ko bude shaguna da sauran wuraren harkoki na yau da kullum a Yankin Babban Birnin Tarayyar Najeriya da ma jihohin Legas da Ogun, matakin ba zai shafi duk wata harka mai alaka da abinci ba.

Amma bisa ga dukkan alamu, a wasu sassan Yankin Babban Birnin na Tarayya, su ma masu sayar da kayan abinci ta shafe su, lamarin da ya jefa wasu ‘yan kasuwar cikin yanayin ana kukan targade sai ga karaya ta samu.

Dalili kuwa shi ne da ma tun kafin wannan doka, Hukumar Birnin ta fara amfani da tsarin takaita harkoki, inda ta bayar da umarnin rufe Kasuwar Wuse da ke tsakiyar birnin Abuja da rukunonin shaguna da ake kira plaza a kwaryar birnin.

Sai dai lamarin bai shafi masu kayan abinci da na sauran kayan masarufi ba a kasuwar ta Wuse, inda aka bar su suna harkokinsu har zuwa ranar Laraba.

Bayan umarnin na shugaban kasa dai, a ranar Litinin jama’a sun yi ta tururuwa zuwa kasuwannin Yankin Babban Birnin na Tarayya da nufin sayayya musamman ta kayan abinci – wannan sayyayya wasu ‘yan kasuwar suka ce ba su taba ganin irin ta ba.

Ta leko ta koma

Bayan nan ne, ranar Talata, wato rana ta farko ta dokar, sai aka wayi gari an garkame kasuwanni ba tare da la’akari da masu sayar da kayan abinci da ke wuraren ba.

Wannan doka ta hada da rukunonin shaguna, wato plaza-plaza da ke garin Kubwa, da Kasuwar Bwari da Kasuwar Karmo, kamar yadda binciken Aminiya ya tabbatar.

Sai dai kuma, daga bisani, a  Bwari ko da yake an rufe kasuwar ita kanta, an kyale masu rumfunan sayar da kayan abinci a wajen kasuwa sun bude.

“Yau dai (Juma’a) ‘yan sanda a karkashin jagorancin DPO na Bwari sun zo suna cewa mutane su tafi gida. To ba mu sani ba ko har da masu kayan abincin suke nufi”, inji Haruna Sara, wani dan kasuwa a garin na Bwari.

Mahauta a daura da Kasuwar Bwari
Wasu mahauta suna gudanar da harkokinsu daura da Kasuwar Bwari da aka rufe

Sannan kuma an samu sassauci a Kasuwar Nyanya a bangaren masu sayar da kayan hatsi wadanda aka bari suna bude rumfunansu tare da sauran masu kayan abinci da ya hada da masu nama, da kaji da kayan miya.

“Dokar ba ta shafi vangaren masu harkan kayan abinci ba”, inji Malam Yau Aliyu, wani mai sayar da kaji a Kasuwar ta Nyanya.

Ita kuwa babbar kasuwar tumatur ta Abuja da ke Deidei, inda ayarin Minista a Hukumar Birnin Tarayya Hajiya Ramatu Aliyu Tijjani ya kai ziyara a ranar Lahadi, an yi mata feshin maganin kashe kwayoyin cuta ne a ranar sannan ta kasance a garkame washegari Litinin saboda a samu damar karasa aikin.

A cewar shugaban kasuwar ta Deidei, Alhaji Adamu Umar Hudu, “Ba mu bude kasuwar ba har a ranar Litinin [saboda muna] tsammanin za a dawo karasa aikin, amma jami’an…ba su dawo ba”.

Saboda haka ne ma harkoki suka koma kamar yadda aka saba a kasuwar, tun daga ranar Talata.

Rumfuna a Kasuwar Wuse
Rumfuna sun kasance a rufe a Kasuwar Wuse tun bayan da dokar ta fara aiki

Haka lamarin ya kasance a kasuwannin kayan marmari da na doya da ke garin Zuba – duk sun kasance a bude kamar yadda dokar ta tanada.

Yanayin ciniki

Wani abu guda da ‘yan kasuwar da a ka baiwa damar yin harkoki a kasuwannin Abuja suka koka da shi, shi ne na karancin ciniki.

Wannan kuwa ba ya rasa nasaba da kaura daga yankin da dimbin jama’a suka yi ta yi tun ma kafin dokar ta fara aiki.

Daga cikin wadanda suka yi tafiyar har da kananan ma’aikatan da ke matakin albashi na 12 zuwa kasa, da kuma tarin masu kananan sana’o’i irin su ‘yan achaba, da masu sayar da ruwa da ‘yan baro da sauransu, inda ta kai wadanda suka saura a galibin wurare ba su da yawa.

Ranar Lahadi 29 ga watan Maris ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya, wanda a cikinsa ya bayyana cewa ya bayar da umarnin hana fita a yankunan da suka fi hadari ta fuskar yaduwar coronavirus.

A jawabin dai ya bayyana wasu bangarori na al’umma da aka daukewa haramcin, ciki har da masu harkokin da suka shafi sarrafa abinci, da raba shi da kuma sayar da shi.