✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

COVID-19: Yawan majinyata zai karu a Kano —Ganduje

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano ya ce akwai yiwuwar adadin wadanda suka kamu da coronavirus ya karu matuka saboda kafa sabbin cibiyoyin gwajin cutar…

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano ya ce akwai yiwuwar adadin wadanda suka kamu da coronavirus ya karu matuka saboda kafa sabbin cibiyoyin gwajin cutar a jihar.

Ganduje ya fadi haka ne yayin wani taron manema labarai da Kwamitin Kar-ta-Kwana a kan Yaki da COVID-19 ya kira ranar Juma’a a Gidan Gwamnati da ke Kano.

Ya kuma ce tuni aka kammala shirye-shiryen kakkafa wasu cibiyoyin gwajin a kananan hukumomi 36 masu nisa daga babban birnin jihar.

“Wajibi ne mu kafa karin cibiyoyin gwaji a kananan hukumomi 36 masu nisa.

“Za mu ci gaba da shiri don gaba, akwai bukatar da an ce kule mu ce cas.

“Za mu tabbatar da cewa an kafa dukkan cibiyoyin da suka dace don kada a mana sakiyar da ba ruwa idan lokacin [bukatar su] ya zo”, inji Gwamna Ganduje.

Ya kara da cewa za a hada karfi da karfe don ganin an kawo karshen annobar COVID-19.

Ya kuma yi kira ga ma’aikatan lafiya da su mayar da hankali ga sauran larurorin da mutane ke fama da su, yana jaddada cewa gwamnatinsa ta bayar da horo ga daruruwan jami’an kiwon lafiya don su yaki cutar ta COVID-19.