✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Crystal Palace ta sake nada Roy Hodgson kociya

Hodgson ya jagoranci kungiyoyi biyar a Firimiyar Ingila.

Crystal Palace ta sake nada Roy Hodgson a matakin kociyanta zuwa karshen kakar bana.

A Juma’ar makon jiya ce Palace ta kori Patrick Vieira, wanda ya maye gurbin Hodgson a Selhurst Park a Yulin 2021, bayan kasa cin wasa a karawa 12 a dukkan fafatawa.

Hodgson, mai shekara 75 ya horar da Watford daga Janairu zuwa Mayun 2022, sannan ya bar kungiyar, bayan da koma buga Championship.

Hodgson ya ce bai taba tunanin sake aikin horar da tamaula da wata kungiyar Firimiya ba, tun bayan da ya bar Watford.

Shi ma Ray Lewington ya sake komawa aikin a matakin kocin Palace da mataimaki, Paddy McCarthy, wanda ya ja ragamar wasan da Arsenal ta ci 4-1 a Firimiyar Ingila ranar Lahadi.

Palace tana ta 12 a teburin Premier da tazarar maki uku tsakaninta da ‘yan ukun karshen teburi, bayan da aka doke ta Emirates.

Wasan da Hodgson zai fara jan ragama a karo na biyu da zai horar da kungiyar shine ranar 1 ga watan Afirilu a gida da Leicester City a Firimiyar Ingila.

Yana da kwarewa a fagen koci na shekara 45, wanda ya horar da Inter Milan da Blackburn da Fulham da Liverpool da West Brom da Palace.

Tsohon kociyan tawagar Ingila ya yi koci a Switzerland da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Finland.

Hodgson ya horar da kungiyoyi shida a Firimiyar Ingila, wanda ya ja ragamar fafatawa 382, kuma shi ne dattijo mai yawan shekara da yake da tarihin koci a gasar.

Ya ja ragamar tawagar Ingila daga 2012 zuwa 2016, wadda ta fice daga karawar rukuni a Gasar Kofin Duniya a 2014, daga nan ya yi ritaya bayan da Ingila ta yi rashin nasara a hannun Iceland a zagayen ’yan 16 a Euro 2016.

A watan Mayun 2022 aka bashi lambar karramawa ta CBE, saboda gudunmuwar da ya bayar a fannin tamaula.