✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Coranavirus ta harbi karin mutum 1,145 a Najeriya

An samu karin mutum 1,145 da cutar Coronavirus ta harba yayin da kuma ta kashe karin mutum 1 a fadin Najeriya. Hukumar Dakile Cututtuka masu…

An samu karin mutum 1,145 da cutar Coronavirus ta harba yayin da kuma ta kashe karin mutum 1 a fadin Najeriya.

Hukumar Dakile Cututtuka masu Yaduwa a Kasar NCDC ce ta sanar da hakan ranar Alhamis da daddare cikin alkaluman da ta fitar kamar yadda ta saba duk rana.

Alkaluman sun nuna an samu karin mutum 1,145 da suka harbu da cutar a jihohi 24 da suka hada da Legas (459), Abuja (145), Kaduna (138), Filato (80), Katsina (70), Gombe (52), Niger (31), Kano (23), Bayelsa (21), Bauchi (18) da Ondo (18).

Sauran su ne Ribas (17), Ogun (12), Oyo (12), Edo (8), Nasarawa (8), Ebonyi (7), Osun (6), Ekiti (5), Kebbi (5), Borno (4), Jigawa (3), Akwa Ibom (2), da Anambra (1).

Ya zuwa yanzu dai cutar ta harbi mutum 76,207 a Najeriya yayin da tuni an sallami mutum 67,110 daga cibiyoyin killace masu cutar bayan samun waraka.

Da wannan sabbin alkaluma da aka fitar, har ila yau jihar Legas ce a kan gaba ta fuskar yawan masu cutar da suka kai 25,895 sai kuma Abuja a mataki na biyu da mutum 9,053 yayin da jihar Kaduna ta tuke a mataki na uku da mutum 4,236.

Haka kuma alkaluman sun nuna jimillar wadanda cutar ta kashe a fadin kasar sun kai 1,201 tun daga bullarta a watan Fabrairun 2020 zuwa yanzu.