✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Coronavirus ta kama Yarima Charles na Birtaniya

Mai jiran gadon sarautar Birtaniya, Yarima Charles, ya kamu da cutar Coronavirus. Wata sanarwa da ofishinsa ya fitar ranar Laraba ta ce Yariman mai shekara…

Mai jiran gadon sarautar Birtaniya, Yarima Charles, ya kamu da cutar Coronavirus.

Wata sanarwa da ofishinsa ya fitar ranar Laraba ta ce Yariman mai shekara 71 da haihuwa ya nuna alamun kamuwa da cutar kuma ya killace kansa a wani gida na masarauta da ke yankin Scotland.

“Gwaji ya tabbatar da cewa Yariman Wales yana dauke da Coronavirus”, inji sanarwar, wadda ta kara da cewa, “Ya dan nuna alamun kamuwa da cutar amma ban da haka yana cikin koshin lafiya, kuma yana aiki a gida a ’yan kwanakin da suka gabata kamar yadda ya saba”.

Sanarwar ta kara da cewa gwajin dai ya nuna cewa maidakin Yariman, Camilla, wacce shekarunta 72 da haihuwa, ba ta dauke da cutar.

Babu bayani a kan yadda aka yi Yarima Charles ya kamu da cutar ta COVID-19.

Kamfanin dillancin labarai na AP ya ambato wata majiya tana cewa “ba zai yiwu ba a tantance wanda yariman ya dauki cutar a wurinsa saboda yawan hidimominsa a ’yan makwannin nan”.

Fadar Buckingham ta ce Sarauniya Elizabeth na cikin koshin lafiya.

“Gani na karshe da Sarauniyar ta yi wa Yariman Wales shi ne a ranar 12 ga watan Maris, kuma tana bin duk wasu shawarwari da suka dace don kiyaye lafiyarta”, inji Fadar ta Buckingham.