✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Covid-19 ta sake harbin mutum 132 a Najeriya

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka a Najeriya (NCDC) ta sanar cewa cutar coronavirus ta sake harbin karin mutane 132 a fadin Najeriya. Hakan na kunshe ne…

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka a Najeriya (NCDC) ta sanar cewa cutar coronavirus ta sake harbin karin mutane 132 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Litinin da daddare, 14 ga Satumban 2020.

A cikin sanarwar da hukumar ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na sada zumunta, ta ce an samu karin sabbin mutane 132 da suka fito daga jihohi 11 na Najeriya kamar haka:

Lagos (52),

Gombe (27),

Plateau (17),

Kwara (10),

Enugu (9),

Ogun (9),

Katsina (3),

Ekiti (2),

Bauchi (1),

Osun (1),

Ribas (1).