✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar COVID-19 ta yi ajalin mutum 15 a Najeriya, 1,303 sun kamu

Alkaluman Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC a ranar Talata sun nuna cewa an samu karin mutum 1,303 sabbin kamuwa da cutar Coronavirus…

Alkaluman Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC a ranar Talata sun nuna cewa an samu karin mutum 1,303 sabbin kamuwa da cutar Coronavirus a fadin Najeriya.

Sanarwar da NCDC ta fitar a shafinta na yanar gizo ta nuna cewa cikin sa’a 24 da gabata, an samu mutum 15 da cutar ta yi ajalinsu.

An samu sabbin kamuwar ne daga wasu jihohi 26 na Najeriya ciki har da babban birnin kasar da suka hadar da; Legas (478), Abuja (211), Nasarawa (83), Ribas (72), Kwara (42), Edo (36), Ondo (34), da Binuwai (32).

Sauran su ne: Kaduna (32), Katsina (26), Filato (26), Kano (25), Taraba (25), Osun (22), Delta (21), Oyo (21), Neja (19), Sakkwato (18), Ebonyi (17), Ekiti (14), Gombe (13), Ogun (12), Bauchi (11), Zamfara (8), Borno (4) da Jigawa (1).

Da wannan sabbin bayanai da Hukumar ta fitar, a halin yanzu cutar Coronavirus ta harbi mutum 124,299 a fadin kasar yayin da kuma jimillar mutane 1,522 suka riga mu gidan gaskiya tun bayan bullar cutar karon farko a wata Fabrairu.

Taskar bayanai ta Hukumar NCDC ta nuna cewa an sallami 99,276 bayan sun warke, inda a halin yanzu mutum 23,501 kacal suka rage masu dauke da kwayoyin cutar a fadin kasar.