✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar ‘Haukan kare’ na kama ’yan Najeriya 55,000 a duk shekara – USAID

Mataimakiyar Daraktan sashen lafiya na Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) a Najeriya, Mieko Mckay ta ce cutar Haukan Kare na kama mutum 55,000 kowacce…

Mataimakiyar Daraktan sashen lafiya na Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) a Najeriya, Mieko Mckay ta ce cutar Haukan Kare na kama mutum 55,000 kowacce shekara a kasar.

Mieko ta bayyana hakan ne a Abuja, yayin kaddamar da shirin kawar da cutar haukan Kare a Najeriya, wanda Ma’aikatar Lafiya da ta Noma da Raya Karkara suka shirya, hadin guiwa da wasu kungiyoyin, domin bikin zagoyowar ranar Yaki da cutr Haukan Kare ta Duniya da aka gudanar ranar Litinin.

A nasa bangaren wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a Najeriya, Walter Mulombu wanda Mataimakinsa Alexander Chimbaru ya wakilta, ya ce ko a baya-bayan nan an samu bullar cutar a jihohin Gombe da Enugu.

Shi ma Ministan Noma da Raya Karkara Mustapha Shehuri, ya ce an samar da shirin ne domin taimaka wa kasashen duniya cim ma nasarar kawar da cutar daga ban-kasa nan da shekara ta 2030.

Da yake gabatar da mukala kan shirin kawar da cutar a Najeriya, Farfesa Junaidu Kabir da ke Sashen Kula da Magungunan Dabbobi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU), ya ce rigafi ga kaso 70 na al’ummar Najeriya, zai taimaka wajen dakile ta, da kuma rage kudin da gwamnati ke kashewa don kau da ita.