✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Cutar Korona ta sake hallaka mutum 10 a Najeriya —NCDC

An sake samun karin mutum 10 da cutar coronavirus ta hallaka a Najeriya cikin sa’o’i 24 da suka gabata kamar yadda Hukumar Kula Cututtuka masu…

An sake samun karin mutum 10 da cutar coronavirus ta hallaka a Najeriya cikin sa’o’i 24 da suka gabata kamar yadda Hukumar Kula Cututtuka masu Yaduwa a kasar NCDC ta sanar.

Duk da ana samun sauki na raguwar mutanen da ke kamuwa da cutar duk rana a Najeriya, sai dai kuma adadin wadanda cutar ke sanadiyar mutuwarsu na hauhawa.

A halin yanzu dai mutum 1,023 cutar ta hallaka a kasar wadda ta fi kowacce yawan al’umma a nahiyyar Afirka bayan samun karin mutum 10 da suka mutu rana daya.

Bayanan da Hukumar NCDC ta fitar ranar Talata ta sanar da karin mutum 239 da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya.

Alkaluman da NCDC ta fitar ranar sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum 19, Filato -116, FCT-33, Ekiti-12, Kaduna-11, Ogun-11, Ebonyi-8, Benue-7, Abia-5, Delta-5, Ondo-4, Edo-3, Imo-2, Osun-2 da Bauchi-1

Cikin sanarwar da Hukumar NCDC ta saba fitarwa duk rana ta bayyana cewa, a halin yanzu mutum 54,247 ne suka kamu da cutar a duk fadin kasar, yayin da tuni mutum 42,010 suka samu waraka, sai kuma mutum 11,214 da suka rage masu dauke da kwayoyin cutar.