✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Kurona: Za a rufe makarantu a jihohin Arewa 9

Gwamnonin Arewa Maso Yamma da Arewa maso Tsakiya sun bayyana aniyarsu na rufe makarantu da ke yankin na kwanaki 30 domin dakile yaduwar cutar Kurona…

Gwamnonin Arewa Maso Yamma da Arewa maso Tsakiya sun bayyana aniyarsu na rufe makarantu da ke yankin na kwanaki 30 domin dakile yaduwar cutar Kurona a yankin.

Gwamnonin sun ce za a rufe makarantun ne daga ranar Litinin 23 ga watan Maris.

Wannan mataki da gwamnonin suka dauka ya biyo bayan kasidar bayan taron da suka yi ne a jihar Kaduna wanda shugaban Kungiyar Gwamnoni ta Arewa maso Yamma, Aminu Masari da shugaban Gwamnonin Arewa ta  tsakiya ‎Sani Bello, suka rattaba hannu kuma aka rabawa manema labarai a jihar.

Jihohin tara sun hada da: Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kwara, Neja, Sakkwato, da Zamfara.

Sun ce, gwamnonin za su dauki matakin ne bayan tattaunawa da hukumar gudanar da jarabawa ta kasa.