✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Kwalara ta barke a Kano

An samu asarar rayukan mutane biyu.

Cutar amai da gudawa da ake kira Kwalara ta barke a wasu kananan hukumomi hudu na Jihar Kano a cewar Ma’aikatar Lafiyar jihar.

Babban jami’in kula da cututtuka masu yaduwa na ma’aikatar, Dokta Sulaiman Iliyasu ne ya tabbatar da hakan a ranar Litinin.

Gidan Rediyon Freedo ya ruwaito Dokta Iliyasu yana cewa, an samu rahoton bullar cutar a Karamar Hukumar Danbatta wadda har aka samu asarar rayukan mutane biyu.

“A watan Afrilu mun samu rahoton bullar cutar amai da gudawa a Danbatta wadda daga nan kuma sai cutar ta bulla a Karamar Hukumar Gwarzo”.

Dokta Iliyasu ya ci gaba da cewa, “Ya zuwa yanzu sama da mutane 25 zuwa 30 ne suka kamu da cutar a kwaryar birnin Kano kamar yadda sakamakon gwajin da muka yi ya tabbatar.”

A cewar jami’in, a yanzu haka Kananan Hukumomin da suka samu bullar cutar sun hada da Karamar Hukumar Dala da Ungoggo, Karamar Hukumar Birni da kuma Tarauni.

Dokta Sulaiman Iliyasu ya bukaci al’umma da su kara kula da tsaftar muhallansu da kuma kai rahoton duk wata cuta da ta bulla ga hukumomin lafiya mafi kusa don daukan matakin gaggawa.