✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Kwalara ta kashe mutum 54, ta kama 604 a Abuja

An dai sami rahoton barkewar cutar a sama da yankuna 120 na birnin.

Minista a Ma’aikatar Babban Birnin Tarayya Abuja, Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu ta ce kimanin mutane 604 ne suka kamu da cutar Kwalara a Kananan Hukumomi shida na birnin, 54 kuma suka rasu.

Ta bayyana hakan ne lokacin da take kaddamar da gangamin wayar da kan jama’a a kan barkewar cutar a birnin.

Ministar, wacce ta kaddamar da gangamin a fadar Agora na yankin Zuba, Muhammed Bello Umar ranar Asabara, ta bayyana matukar damuwarta kan karuwar masu dauke da cutar a yankin.

Hajiya Ramatu ta ce an sami rahoton barkewar cutar a sama da yankuna 120 na Kananan Hukumomi shida na babban birnin.

A cewarta, Karamar Hukumar Birnin Abuja da kewaye ce ke kan gaba wajen yawan wadanda suka kamu, sai kuma Gwagwalada da Bwari da suke biye mata baya.

Daga nan sai ta yi kira ga jama’a da su tabbatar da tsaftar muhallansu tare da tabbatar da zubar da shara a inda ya dace don takaita yaduwarta.