✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Cutar Kyandar Biri ta bulla a Katsina

An samu bullar cutar Kyandar Biri a Katsina kamar yadda gwamnatin jihar ta tabbatar.

An samu bullar cutar Kyandar Biri a Katsina kamar yadda gwamnatin jihar ta tabbatar.

Gwamnatin ta tabbatar cewa cutar ta harbi mutum daya yayin da ake dakon sakamakon wasu samfura 15 daga dakin gwaje-gwaje da aka kai Abuja, babban birnin kasar.

Kwamishinan Lafiyar jihar, Yakubu Nuhu Danja ne ya tabbatar da hakan ranar Talata yayin kaddamar da shirin rarraba magunguna kyauta da kuma cibiyar kiran nema agajin gaggawa a Ofishin Hukumar Lafiya a Matakin Farko na jihar.

“Mun tabbatar da cewa cutar kyandar biri ta harbi mutum daya kuma an dauki dukkan matakan da suka dace na yi wa marar lafiya magani da tuni an sallame shi.

“Muna da wasu mutum 15 da aka zargin sun kamu da cutar wadanda aka kai samfurin jininsyu dakin gwaje-gwaje da ke Abuja.

“A yanzu haka muna sa ran sakamakon gwaje-gwajen zai fito nan da mako guda,” a cewarsa.

Dangane da aikin rarraba magunguna da gwamnatin jihar ta kaddamar, Kwamishinan ya ce hakan wani mataki na tunkarar yiwuwar barkewar cututtuka da galibi akan samu a irin wannan lokaci na damina.

“A yanzu haka mun tanadi rigakafin magance annobar cututtuka irinsu cutar Sankarau, Kyanda da Kwala.”