✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cutar Murar tsuntsaye: An kashe kaji 329,556 a gidajen gona 62

Wata majiya daga Ma’aikatar Gona da Raya Karkara ta Kasa ta tabbatar da cewa akalla kaji 329,556 ne aka kashe .

Gwamnatin Tarayya ta ce ta kashe kaji sama da 329,556 a gidajen gona 62 bayen samun rahoton barkewar annobar cutar Murar Tsuntsaye a sassa da dama na Najeriya.

Cutar dai wacce aka ba da rahoton barkewarta tun ranar 29 ga watan Janairun 2021 na ci gaba da barazana ga masu kiwo da masu gidajen gona.

Daga watan na Janairun dai zuwa biyar ga watan Afrilu, kimanin kaji 421,947 ne suka kamu da cutar samfurin H5N1, wacce yanzu ta fantsama zuwa Kananan Hukumomi 20 a jihohi takwas na Najeriya.

Wata majiya daga Ma’aikatar Gona da Raya Karkara ta Kasa ta tabbatar da cewa akalla kaji 329,556 ne dake gidajen gona 62 a jihohin da cutar ta bayyana aka kashe .

Babban jami’i mai kula da sashen lafiyar dabbobi a ma’aikatar, Dakta Adeniran Alabi ya ce kusan shekaru biyu kenan Najeriya ba ta sami rahoton bullar cutar ba in banda ranar 29 ga watan Janairun da aka sami rahoton bullarta a Karamar Hukumar Nassarawa ta jihar Kano.

Ya ce babbar hanyar da suke bi wajen yaki da cutar a yanzu ita ce ganowa, kashewa, yin feshi da kuma biyan diyya ga masu gidajen gonakin.

“Muna kira da babbar murya ga masu gidajen gona da su dauki dukkan matakan da suka kamata wajen dakile ci gaba da yaduwar cutar zuwa gonakinsu,” inji Mista Alabi.

Ya kuma ce ma’aikatarsu ta jima tana gudanar da feshi a kan tsuntsaye da kaji masu rai a kasuwannin kajin jihohin da cutar ta bulla, wacce ya ce ita ce babbar hanyar dakile ci gaba da bazuwarta.

Babban jami’in ya kuma ce Ma’aikatar Gonar na aiki kafada da kafada da Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya (NCDC) wajen daukar samfurin kwayar cutar a jikin mutanen da ke aiki a irin wadannan gidajen gonar domin fadada bincike a kai.