✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Cuwacuwa ta fi yawa a daukar ma’aikata 774,000’

Jam’iyyar PDP ta yi zargin ware wa masu rike da mukaman siyasa gurabun daukar kananan ma’aikatan wucin gadi 774,000 na Gwamnatin Tarayya. A kwanakin baya…

Jam’iyyar PDP ta yi zargin ware wa masu rike da mukaman siyasa gurabun daukar kananan ma’aikatan wucin gadi 774,000 na Gwamnatin Tarayya.

A kwanakin baya ne Minista a Ma’aikatar Kwadago Festus Keyamo ya rantsar da ’yan kwamitin da za su zabi ma’aikatan a jihohi.

Ma’aikatan za su yi ayyukan shara da gadi da dangoginsu na tsawon wata uku inda a kowacce daga kananan hukumomin kasar 774 za a dauki mutum 1,000.

Amma PDP na zargin gwamnatin APC da cuwacuwa a daukar ma’aikatan wanda ta ce babban zalunci ne ga marasa aiki a Najeriya.

“Tun da kudin gwamnati za a biya su to bai dace a sa siyasa a ciki ba ta yadda dukkannin ’yan Najeriya za su samu dama ba tare da la’akari da alakarsu ta siyasa, addini ko kabila ba.

“PDP na Allah-wadai da yadda aka ware 800 daga cikin gurabu 1,000 na ayyukan a kananan hukumomi ga ’yan siyasa; sauran 200 kuma an bar wa mutane, ciki kuma har da ’yan siyasa.

“Hakan da gwamnatin APC ta yi zalunci ne, kuma zai iya kawo kiyayya a kasa, don haka muke kira da ta gaggauta janye wannan mataki domin amfanin ’yan kasa”, inji Sakatare Watsa Labaran PDP na Kasa, Kola Ologbondiyan.

Wakilinmu ya tuntubi shugabannin APC domin jin abun da za su ce, amma ba su riga sun ce komai game da zargin ba tukuna.

Gwamnatin Tarayya ta ware biliyan N52 domin biyan ma’aikatan da za su yi aikin a kasafin kudi na 2020.