✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da Dumi-dumi: Sarkin Zazzau Shehu Idris ya rasu

Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya rasu yana da shekara 84

Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, rasuwa yana da shekara 84 a duniya.

Sarkin ya rasu ne da misalin karfe 12 na ranar Lahadi a Asibitin Sojoji da ke Kaduna.

Wazirin Zazzau Alhaji Ibrahim Aminu ne ya tabbatar wa Aminiya rasuwar.

Daya daga cikin sarakuna mafi dadewa a kan karaga, a watan Fabrairu ya yi bikin cika shekara 45 yana mulki.

An haifi Alhaji Shehu Idris ne a 1936, kuma ya rike mukamai da dama a Najeriya.

Marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris lokacin da aka nada shi ranar 11 ga watan Fabrairun 1975

Daga cikin mukaman da ya rike akwai Shugaban Hukumar gidan Rediyo da Talabijin ta Jihar Kaduna (KSBC), da Darakta a Hukumar Gudanarwa ta kamfanin UAC.

Ya kuma yi aiki da Baitulamalin Hukumar En’e ta Zariya, da Ma’aikatar kananan Hukumomi ta Jihar Arewa a matsayin sakatare, sannan ya rike sarautar Danmadamin Zazzau Hakimin Zariya daga 1973 zuwa 1975.