✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Da gangan aka kirkiri Boko Haram don a wargaza Najeriya – Buhari

Ya ce yanzu hankali ya koma kan sake gina yankunan

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi zargin cewa da gangan aka kirkiri kungiyar ta’addanci ta Boko Haram domin a ga bayan Najeriya.

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin mambobin Kungiyar Limaman Darikar Katolika ta Najeriya (CBCN) a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja ranar Laraba, kamar yadda Kakakin Shugaban, Femi Adesina, ya fada a cikin wata sanarwa.

Buhari ya ce akidar ’yan ta’addan, wacce ke kokarin hana mutane neman ilimi gurbatacciya ce da ke kokarin hana ci gaba.

Shugaban ya kuma ce zai kara mayar da hankali kan nasarorin da ya samu a bangaren tsaro a mulkinsa, kamar yadda zai yi wa bangaren tattalin arziki kafin ya mika mulki ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa.

Ya kuma ce an samu gagarumar nasara a bangaren tsaro, musamman a yankin Arewa maso Gabas, inda ya ce a yanzu hankali ya karata ne kan sake gina yankin.

Shugaba Buhari ya kuma shaida wa Limaman cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali sosai wajen sake farfadowa da kuma gina yankunan da ayyauakn ta’addanci ya daidaita, inda ya kuma ce babu wani bangare na kasar da yake karkashin kulawarsu a yanzu.

Dangane da batun tattalin arziki kuwa, Buhari ya ce yanzu haka masu zuba jari na da cikakken kwarin gwiwa a kan kasar.

Sai dai ya koka kan yadda ya ce zagon kasan da ake yi ta hanyar kai hare-hare a wuraren hakar mai da kuma satar shi kansa man sun taimaka wajen rage yawan kudaden shigar da kasar ke samu a halin yanzu.

A nasa jawabin, Shugaban Limaman, Rabaran Lucius Iwejuru Ugorji, ya yaba wa Buhari kan ayyukan ci gaban da ya kawo, musamman rattaba hannu a kan Kudurin dokar Zabe.

Daga nan sai ya roke shi da ya yi amfani da ragowar watannin da suka rage masa a ofis wajen dada bunkasa tsaro da kuma tattalin arziki.